Karin albashin 'yan sandan Najeriya
November 27, 2018To haka kwatsam ne dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sanar da amincewarsa na a karawa 'yan sandan Najeriyar albashi da alawus-alawus dinsu bisa tsari na basu ingantaccen albashi a kasar, abin da ya sa ran kawo karshen dadewar da 'yan sandan suka yi suna koke na karancin albashin da suke karba.
Duk da cewa Malam Kabiru Adamu masani a fanin tsaro ya ce lamarin zai yi tasiri, amma matsalar 'yan sandan Najeriyar ta wuce batu na karin albashi.
Rashin kyautata wa 'yan sandan dai ana kallonsa a matsayin dalilin dake kawo koma bayan da ake fuskanta a aikinsu, inda daga Zamfara zuwa Legas, da Kaduna da ma yankin Niger-Delta sojoji ne ke aikin da ya kamata a ce 'yan sandan na yi.
Fatan samun sauyi mai ma'ana
Duk da cewa ba a kai ga bayyana ko nawa ne aka kara wa 'yan sandan ba a matsayin dabara ta kauce wa fuskantar hauhawar farashin kaya.
Tuni hukumomin 'yan sanda suka bayyana cewa za a ga canji. Malam Bala Ibrahim shi ne mai baiwa sifeto janar na 'yan sandan Najeriya shawara a fannin yada labaru.
"Tuni sifeto janar ya aika sako ga rundunar 'yan sanda da ke kula da jihohi, yana bayyana musu cewa shugaban kasa ya sahale musu abin da suka jima suna nema. Yanzu ana sauraron ganin yadda za su sake zage damtse, kuma nan ba da jimawa ba zai kira taron rundunar ta kasa baki daya domin ya ja musu kunne."
Fatan samun sauyi da ake da shi ga aikin 'yan sanda ya sanya laluben matakin da ya kamata a dauka ga 'yan sandan Najeriyar da adadinsu ya zarta dubu 370 ga al'ummar Najeriyar mai mutane kusan miliyan 200.
A yayin da ake wannan dan takarar neman shugabancin Najeriyar a karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar na koken cewa an yi karin ne don bukatu na siyasa, abin da gwamnatin Najeriyar ta musanta. Al'ummar kasar na cike da fatan samun sauyi daga 'yan sandan kasar ta fannin yakar masu aikata miyagun laifufuka da suka addabi kasar.