Tarihi
Najeriya: Tarihin jami'ar jihar Kaduna
November 26, 2018
Talla
An kirkiro jami'ar jihar Kaduna wacce ake kira Kaduna State University ko KASU a takaice a shekara ta 2004 a lokacin gwamnatin Alhaji Ahmed Muhamed Makarfi. Ta fara da bayar da karatun sharar fage da ake kira College of Basic and Remidial Studies kafin a shekara ta 2005 ta soma bada izinin soma karatun digiri. Parfesa Sambo shi ne shugaba na farko na wannan jami'a. Ku saurari dai cikakken bayani daga bakin Farfesa Abdullahi Ashafa masanin tahiri kana daya daga cikin mataimakan shugabar jami'ar ta Jihar Kaduna.