1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Twitter da gwamnatin Najeriya

June 10, 2021

Sannu a hankali rikicin gwamnatin Najeriyar da kamfanin Twitter na kara kamarai, inda ma rikicin ke shirin shafar sauran kafafen sadarwa na zamani a Tarayyar ta Najeriya.

https://p.dw.com/p/3uj0u
Symbolbild | Twitter
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Skolimowska

Mahukuntan Tarayyar Najeriyar dai, sun ce dole ne kamfanin na Twitter da ma ragowar kamfanonin sadarwa na zamani, su yi rijista a kasar kafin samun damar shiga kasuwar Najeriyar. Wannan matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka dai ya nuna harzukar da gwamnati ta yi a fili, bayan da kamfanin sadarwar na Twitter ya goge wani rubutu da shafin shugaban kasar ya yi, inda yake barazana ga masu rajin raba kasar.

Matakin gwamnatin dai ya janyo mabambantan ra'ayoyi a tsakanin al'ummar kasar, inda aka samu masu goyon bayan matakin da kuma masu adawa da shi suna masu ganin take 'yancin fadar albarkacin baki ne.