1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani kan haramta kungiyar 'yan Shi'a a Najeriya

Uwais Abubakar Idris MNA
July 29, 2019

Haramta kungiyar ‘yan Shi’a tare da ayyanata a matsayin kungiyar ta’adda da gwamnatin Najeriya ta yi ya haifar da kace nace.

https://p.dw.com/p/3MuNa
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Ta bayyana a fili cewa dai tura ta kai bango a bangaren gwamnatin Najeriya da ta kai ga daukan wannan mataki ta hanyar amfani da kotu a kan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Najeriya wato IMN da aka fi sani da 'yan Shi'a. Tun da dadewa aka hango take-taken kaiwa ga hakan bisa munin zanga-zangar da 'ya'yan kungiyar ke yi da ta kai ga rasa rayuka. To sai dai ga kakakin kungiyar Muhammad Gamawa ya ce da fa sakel.

"Mu ba mu dauka cewa akwai wata kotu da za ta hana mai addini ya yi addinisa ba, ayyukan ta'addancin kuma muma kanmu mun sha wahala da 'yan ta'adda, tun da Boko Haram sun kashe mana mutane da dama kusan shekaru biyar da suka wuce. Hakika za mu daukaka kara."

Tuni dai gwamnatin ta bakin mai bai wa shugaban kasar shawara a fannin yada labaru Garba Shehu ya sanar da cewa su basu hana kungiyar yin addini ba, kuma sun haramtata ne saboda kaucewa ci gaba da rikici da tada hankali. Shin me dokokin Najeriya suka tanada a kan daukan irin wannan mataki? Barrister Mainasara Umar masanin harkokin shari'a ne da ke Abuja.

Baya ga asarar rayuka an kuma yi kone-kone a zanga-zangar da 'yan Shi'a suka yi baya bayan nan a Abuja
Baya ga asarar rayuka an kuma yi kone-kone a zanga-zangar da 'yan Shi'a suka yi baya bayan nan a AbujaHoto: Reuters/P. Carsten

"Sashe na biyu na dokar hana ta'addanci a Najeriya ta 2013 ta yi bayanin cewa duk wani wanda ya yi wani abu da ya kawo ma wani firgici, aiki ne na ta'addanci. Sashe na 45 ya kawo tarnaki na cewa idan abubuwan da kuke yi zai shafi hakkin wasu 'yan Adam ana iya hana ku ko kuma dakile wannan abin."

Sanin cewa ko da a shekara ta 2016 gwamnatin jihar Kaduna ta haramta kungiyar kuma ma akwai kungiyoyi irin na Boko Haram da na 'yan awaren Biafra da duka aka dauki irin wannan mataki a kansu. Ko za a ce wannan zai iya zama hanyar samun mafita? Mallam Kabiru Adamu masani ne a fannin tsaro da ke cibiyar Beacon a Abuja.

"Zai yi wuya a ce haka nan domin ita kungiyar tana ikirarin cewa tana harkokinta ne saboda akida. Amfani da doka don ka danne akidanci bai taba yin nasara, shi ya sa tuntuba da kuma tabbatar da cewa an fahimtar da shugabannin kungiyar na alfanun bin doka ita ce kadai hanya mafita."

Dangantakar kungiyar 'yan Shi'a da gwamnatin Najeriya dai ta dauki sabon salo ne tun daga 2015 lokacin da 'ya'yan kungiyar suka yi arangama da sojoji a garin Zaria. Yanzu za a sa ido a ga abin da zai biyo bayan matakin da gwamnatin ta dauka kan kungiyar.