Najeriya ta maka kungiyar ASUU a kotu
September 12, 2022Kotun sasanta ma'aikata a Najeriya, ta dage sauraron karar da gwamnatin kasar ta kai kungiyar malaman jami'o'i ASUU inda take kalubalantar ci gaba da yajin aikin da kungiyar malaman ke yi. Gwamnatin Najeriyar dai na bukatar kotun ne da ta tilasta masu komawa bakin aiki. Gwamnatin Najeriyar dai ta maka kungiyar malaman jami‘o'in ne a kotu a kan dagewa da ma cijewar da suka yi na ci gaba da yajin aiki da ya shiga watani bakwai a yanzu, abin da ya gurgunta daukacin tsarin karatun jami‘o'in gwamnati a kasar.
Alkalin kotun mai shari'a Hamman Polycarp, ya saurari mahawarorin da aka tafka a tsakanin lauyoyin da ke kare gwamnati da ta shigar da kara da na kungiyar malaman jami‘o'i ta ASUU da fitaccen lauyan nan mai kare hakkin jama'a Femi Falana ke kare su.
Tun kafin wannan lokaci sai da gwamnatin ta yi kokari na ingiza dalibai su kai malaman nasu kara a kan yajin aikin, abin da daliban suka yi biris da shi sanin dangantakar da ke tsakaninsu da malaman nasu.
Lauya Femi Falana dai ya bayyana cewa wannan wani kokari ne na jan kafa da jinkirta daukacin al'amarin da yanzu yake gaban kotu sanin yadda shari'a take a Najeriyar.
Kungiyar kare hakin jama'a ta SERAP dai ta bayyana a kotun inda take neman lallai sai a sanyata a cikin jerin wadanda ke a cikin shari'ar. Lauyan kungiyar Ebun Olu Adegboruwa ya shaida wa kotun cewa SERAP ta shigar da kara a kotun tana son a tilasta wa gwamnatin Najeriya ta mutunta yarjejeniyar da ta cimmawa da kungiyar a shekarar 2019, amma lauyan gwamnati ya ki amincewa da wannan bukata.
Mai shari'a Hamman Polycarp, ya ce shi alkali ne na wannan lokaci da kotuna ke hutu ya san za a mika shari'ar ga wani alkali daban, ya bukaci dukkanin bangarorin su tsara takardunsu inda ya dage shari'ar zuwa ranar Juma'a 16 ga watan nan na Satumba.