1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sojoji na nan daram a yankin IPOB

September 15, 2017

Gwamnan Jihar Abia na cewar za a janye dakarun soji da ke sintiri a sassan Jihar, sai dai rundunar soji kuma da ta tabbatar da afkawa gidan Jagoran 'yan aware na IPOB Nnamdi Kanu, ta ce sintirin sojoji yanzu suka fara.

https://p.dw.com/p/2k3pk
Nigeria Soldaten in Damboa
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

A yammacin Alhamis ne gwamnan Jihar ta Abia yayi wa Jama'ar jihar tasa jawabi na musamman, inda yake cewar za a janye sojojin da aka turo don atisayen dakarun damisa na Python Dance 2 a Jihar da ke zaman mahaifar Nnamdi Kanu, wato Jagoran kungiyar IPOB ta 'yan a raba kasa. Gwamnan dai ya ce yanayin tsaro a jiharsu a 'yan kwanakin nan da ya yi jallin auno karin jami'an tsaro zuwa jihar hakan kuma ya haifar da damuwa sosai, don haka ya tuntubi jami'an tsaro na sojoji wadanda a cewarsa sun ba shi tabbaci na janyewa bayan tuntubar da ya yi wa shugaban kasa.

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

To sai dai daga bisanin bayanin na gwamna cewar za a janye sojoji daga jihar, rundunar sojin Najeriyar ta ce ba wata maganar janye dakarunsu kamar yadda mataimakin babban daraktan yada labarai na rundunar sojojin Najeriya da ke runduna ta 82, wato kanal Sagir Musa ya tabbatar wanda ya ce a simame da suka kai gidan Kanu sun gano tarin makamai baya ga ikirari na zama shugaban kasa, an kuma kama wasu na kusa da shi .

Kimanin dai 'yan rajin na Biafra sama da 30 ne ke tsare a gidan yari a jihar Rivers suna fuskantar sharia.

Tuni dai ainihin kungiyar rajin kafa kasar Biafra ta MASSOB, wadda ita ce ta yaye kananan kungiyoyin rajin na Biafra irin su IPOB, da kuma ke ikirarin ita hanyar lallama take bin al'ammurranta, ta yi Allah wadai da yadda kungiyar IPOB din ta Nnamdi Kanu ke neman yamutsa daukacin Najeriya.