1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gwamna a jihar Ondon Najeriya

October 9, 2020

Al'ummar jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, na shirin kada kuri'unsu a zaben gwamna da za a gudanar a Asabar din karshen mako.

https://p.dw.com/p/3jiDF
Nigeria Vizepräsident Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo tare da gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Odunayo AkeredoluHoto: Novo Isioro

A ranar Asabar 10 ga watan Oktobar wannan shekara ta 2020 da muke ciki ne dai, al'ummar ta jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, za su kada kuri'unsu a zaben na gwamna, zaben da tuni 'yan takara da magoya baynasu suka shirya masa. Jami'an tsaro sun bayyana cewa a shirye suke domin tabb atar da ganin an gudanar da zaben cikin lumana, inda tuni suka cafke duk wasu masu shirin tayar da rikici, wato kwatankwacin abin da ya faru a wasu jihohi misali jihar Edo.  Manyan jam'iyyun kasar na APC da PDP  ne dai, ake sa ran za su taka rawar azo a gani yayin zaben, kuma sun nuna cewa a shirye suke kuma cike da fatan ganin sun yi nasara. Tuni dai hukumar zaben kasar mai zaman kanta, wato INEC ta shirya domin gudanar da zaben.