1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun sakar bangaren sabuwar PDP da APC

Uwais Abubakar Idris | Abdul-raheem Hassan
June 5, 2018

‘Yan tsohon bangaren sabuwar PDP da ke cikin babbar jam'iyyar gamayyar APC sun janye daga tattaunawa da fadar shugaban kasa bisa zargin cin fuska.

https://p.dw.com/p/2yxze
Nigeria Präsident Muhamadu Buhari
Hoto: Novo Isioro

Duk da lashe aman da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi na janye gayyatar shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki don amsa tambayoyi kan zargin alaka da wasu 'yan bindiga da aka kama a garin Offa na jihar Kwara, amma 'yan sabuwar PDP na cewa babu sulhu bayan da aka janye wa shugabannin majalisun biyu wasu jami'an tsaron farin kaya.

Malam Lauwali Shu'abu shi ne shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso Gabashin Najeriya da ke cewa:

"Siyasa ta gaji bambancin ra'ayi, ba wai bangaranci ba. Ba ma tsoron ficewarsu. amma kuma ba mu so su bar jam'iyyar."

Tuni dai batun janye jami'an tsaron da ke kare shugaban majalisar dattawan ya sanya jam'iyyun adawa maida martanin nuna fargabar jefa demukuradiyyar Najeriya cikin mawuyacin hali.

Nigeria Regierungspartei PDP
Alamar babbar jam'iyyar adawa a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Malam Shehu Kura shi ne kakakin shugaban jam'iyyar PDP wanda ya ce:

"Wannan abin takaici ne, abin da gwamnatin APC ke yi ba zai taimaka wa demokuradiyya da komai ba illa koma baya, saboda akwai alamar tozarci. Fatanmu shi ne jam'iyyar APC su kiyaye ka'idojin demokuradiyya."

A yayin da ake ganin alamun komawar hannun agogo baya ga jam'iyyar, APC na kokarin shawo kan 'ya'yan sabuwar PDP.

Abin jira a gani shi ne yadda za a shawo kan matsalar kamin lokacin zaben shekara ta 2019.