1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar adawa ta PDP za ta saka ido kan zaben gwamnoni

Uwais Abubakar Idris
March 4, 2019

Bayan kammala taron jami'an jamiyyar a Abuja ne ta yi kashedin tura sojoji a zaben gwamnonin da ‘yan majalisun dokoki da za’a yi tare da daukan matsaya a kan sakamakon zaben shugaban kasa da ta sha kaye a cikinsa.

https://p.dw.com/p/3EQv3
Nigeria, ehemaliger Vizepräsident Atiku Abubakar
Hoto: Getty Images/P.U.Ekpei

Wannan shi ne taron farko da jamiyyar ta yi da daukacin manyan jami'anta tun bayan zaben shugaban kasa na Najeriya da jamiyyar ta ce ba ta amince da shi ba, bisa zargin da ta yi na cewa an tafka magudi. Manyan jami'an jam'iyyar sun kwashe sao'i da dama suna tattaunawa a asirce a kan batutuwa da dama da suka hada da kame surukin mutumin da ya tsayawa jam'iyyar takara da lauyansa.

Tun da farko, sai da shugaban jamiyyar Uche Secondus ya yi jawabi ga mahalarta taron a fusace bisa abinda ya faru a zaben shugaban kasan Najeriyar da ya ce suna gargadi kada a kuma irinsa. A game da zaben gwamnonin da ‘yan majalisar dokoki da za'a yi a ranar Asabar mai zuwa.

Taron dai ya samu hallartar manyan jami'an jamiyyar har da dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa Atiku Abubakar da magoya bayansa suka rinka murna da sake ganinsa tun bayan fitar da sakamakon zaben shugaban kasa da Muhammadu Buhari ya yi nasara.