1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP ta kafa sabuwar jam'iyyar kawance

Ramatu Garba Baba
July 10, 2018

Jam'iyyar adawa ta PDP ta sanar da kafa jam'iyyar kawance da ta yi wa lakabi da Coalition of United Political Party ko CUPP, inda ta ce za ta sanar da sunan wanda za ta tsayar takarar kujerar shugaban kasa na 2019.

https://p.dw.com/p/317RV
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Tom Ikimi, daya daga cikin 'ya'yan jam'iyyar ta PDP,  da ya yi wa manema labarai karin bayani a Abuja, ya ce sun cimma yarjejeniya da sauran jam'iyyun kuma za su tsayar da dan takara daya tilo a zaben shugaban kasar.

A na ganin wannan wata babbar barazana ce ga jam'iyyar ta APC mai mulki da ke kuma fatan ci gaba da jan ragamar mulki. A makon da ya gabata, wani bangare na jam'iyyar APC mai mulki, ya ayyana ballewar 'yan APC ta masu neman sauyi da aka yi wa lakabi da Reformed APC.

Karkashin dokokin hukumar zaben Najeriya, a na son duk wata jam'iyya ta kammala tsayar da 'yan takararta na neman kujerar shugaban kasar a tsakanin sha takwas ga watan Augusta zuwa bakwai ga watan Oktoba da wa'adin ke cika.