1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Martani kan tallafi ga talakawa

August 18, 2023

Al'ummar Najeriya na yin martani kan tallafin da gwamnatin ta ce za ta ba kowacce jiha don rage radadin cire tallafin man fetur. Gwamnatin ta ce za ta ba kowacce jiha Naira milliyan dubu biyar don sayen kayan masarufi.

https://p.dw.com/p/4VL4n
Tallafin abinci ga talakawa a Najeriya
Tallafin abinci ga talakawa a NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Gwamnatin tarayyar ta umarci jihohi su yi amfani da kudaden tallafin wajen sayen buhun shinkafa 100,000 da masara buhu 40,000 da kuma taki. wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin tarayya ke ba da irin wannan tallafin jinkai ba, amma talakawa na kokawa cewa ba ya zuwa garesu saboda 'yan siyasa na yin babakere a kai. A jihar Zamfara wadda hare-haren 'yan bindiga ya tagaiyara tattalin arzikinta al'ummar na nuna fargaba kan tallafin.

Sai dai gwamnatin jihar ta bakin kakakinta Mustafa Jafaru Kaura ta ce tun kafin tallafin gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai raba tallafin da ta samarwa al'ummarta kuma za a yi wa kowa adalci

Mata na daga wadanda ke koken tallafin idan an bayar da suka ce baya zuwa garesu saboda suna cikin gidaje ba'a tunawa da su sai lokacin jefa kuri'a .

Ita ma a nata bangaren gwamnatin jihar Katsina ta ce tuni ta yi tanadi tun kafin tallafin gwamnatin tarayyar kamar yadda Abubakar Badaru Jikamshi mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan kafafen watsa Labaru ya yi wa DW  Karin bayani

Ko shakka babu cire tallafin man fetur da mahukuntan Najeriya suka yi ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali inda rahotanni ke nuna yanzu haka akwai mutanen da basa samun abincin su da iyalansu. To ko wannan tallafin zai magance matsalolin abinci.