1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya : Radadi bayan janye tallafin man fetur

Uwais Abubakar Idris AMA
November 24, 2021

Gwamnatin Najeriya ta tsara biyan marasa karfi sama da milyan 30 Naira dubu biyar domin rage masu radadin janye tallafin man fetur da ta ke shirin yi a tsakiyar shekarar 2022.

https://p.dw.com/p/43QQJ
Erdöllraffinerie in Nigeria
Matatar man fetur ta jihar Kaduna da ke arewacin NajeriyaHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Bayan dogon lokaci tana jan kafa da hasashen abinda ka iya biyo baya, daga karshe gwamnatin Najeriya yanke shawarar janye tallafin man fetir da take biya da ya zarta dalla bilyan 30 a kasar, tallafin da ya zama babbar kafar da aka dade ana zargin cin hanci da rashawa da sunan ‘yan Najeriya, matakin da ya zamewa kasar dole tun bayan amincewa da sabuwar dokar man fetir ta PIA. Katse hanzari ko toshe kofar tsirarun jami’an gwamnati da suka huda suka ga da jinni, abinda ya sanya kafa bakinsu suna tsotsa da sunan tallafin man fetir a kasar.

Karin Bayani : Najeriya kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka

Nigeria Tankstelle in Lagos
Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

To sai dai akwai masu tababar wanzauwar tallafin man na Najeriya domin tun a watan Afrilun shekarar 2020 gwamnatin da kanta ta sanar da dakatara da biyan kudin tallafi. Comrade Isa Tijjani tsoshon sakataren kungiyar Nupeng kuma kwarare a wannan fanin. "Duk wanda ya ce zai janye talafin mai a yayin da matatunmu basa aiki to tatsuniya ce yake ko kuma wasa da hankali ne, ai dan Najeriya abinda ya fi damunsa shi ne ya samu man fetir cikin sauki, idan matatun manmu na aiki duk wadannan abubuwan na kawo mai daga waje karewa zai yi, ba wani dan kasuwar da aka sahalewa ya kawo mai daga waje dan a biya shi wannan tallafin, kawai yaudara ce."  Hangen dalla da akan ce ba shiga birni ba a game da tallafin man fetir din Najeriyar, domin gwamnatin ta sanar da daukan wannan mataki ne duk da cewa matattun man kasar suna a durkushe sai dai hasashe na gyara da ma fara aikin sabbi da ‘yan kasuwa ke ginawa irin su Aliko Dan Gote, anya Najeriyar ta shiryawa lamarin?

Karin Bayani : Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai

Nigeria Benzin Schwarzmarkt
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Owolabi

A bayyane take a fili janye tallafin zai sanya man fetir yin tsada a Najeriyar, inda kamfanin albarkatun main a kasar ya dade da hasashen zai iya kai Naira 400 kowace lita guda, wannan ya sanya gwamnatin tsara baiwa marasa galihu milyan 30 zuwa 40 talafin kudin shiga mota na Naira dubu biyar. Bankin duniya ya dade da nuna cewa tallafin mai ne ke yiwa Najeriya tabaibay, abinda za’a sa a ga jnaye tallafin zai zaburara da tattalin arzikin Najeriya. Najeriyar dai a yanzu na cikin kalubale na janye tallafin da tsoron karuwar farashin mai da ya zama dole a kasar da ke da arzikin mai amma ta dogara da shigo da shi daga kasashen waje saboda zargi na cin hanci da ya sanya gaza gyara matattun man kasar da ma gina sabbi.