1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta hana belin jagoran 'yan shi'a

Ramatu Garba Baba
November 7, 2018

Kotu a Najeriya ta ki amincewa da bukatar da aka shigar a gabanta ta bayar da belin Sheikh Ibrahim Zakzaky, jagoran kungiyar 'yan uwa musulmi ta 'yan Shi'a da ake tsare da shi tun a shekarar 2015.

https://p.dw.com/p/37quj
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Alkalin kotun da ke jahar Kaduna, Justice Gideon Kurada ya ce malamin ba ya fuskantar barazana ta fannin lafiya da zai saka a bayar da belinsa kamar yadda ya nemi a yi.

Wannna dai shi ne karon farko da Malam Zakzaky ke baiyana a gaban kotu tun bayan arangama a tsakanin mabiyansa da jami'an tsaron Najeriya a Abuja a kwanakin da suka gabata, inda mutum fiye da arba'in suka rasa rayukansu.Tun a watan Disambar shekarar 2015 ne ake tsare da Zakzaky bayan wani artabu a tsakanin mabiyansa da sojojin kasar a garin Zariya na jihar Kaduna da ke arewacin kasar inda mutane da dama suka rasu.