1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin kawo karshen rikicin kudancin Kaduna

January 6, 2017

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da izinin daukar dukkanin matakan da suka dace domin kawo kashen rikice-rikicen da ke addabar daukacin yankin Kudancin Kaduna.

https://p.dw.com/p/2VPLM
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

 

Wannan na kunshe ne cikin wata takardan da aka rarraba wa manema labarai wanda Mai baiwa shugaban kasa shawarwari kan harkokin watsa labarai Alhaji Garba shehu ya sanya wa hannu, inda ya ce Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta damu ainun gami ga karuwar tashe-tashen hankulan da suka dade suna janyo asarar rayuka da dunbun dukiyoyi tare da sanya jama'a fadawa cikin matsalolin rayuwa, wanda hakan ya sanya gwamnatin ba da umurnin tabbatar da ganin cewa anyi dukkanin maiyiwuwa dan magance sake aukuwar rigimar kudancin na Kaduna.

Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
'Yan sandan Najeriya masu sintiriHoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Alhaji Garba shehu ya ci-gaba da cewa a makon da ya gabata ne Gwamnati ta aike da shugaban ‘yan sandan Najeriya don kai ziyarar gani da idanu a dukkanin kauyukan da rigingimun suka shafa sakamakon ayyukan ‘yan bindiga, wanda shugaban ‘yan sandan IG Ibrahim Idris da sauran kwamnadojin tsaronsa suka ga cewa ya kamata a kafa wata cibiyar kwantar da tarzoma ta jami'an tsaro a yankin, wadda za ta kumshi kimanin ‘yan sanda sama da 700, dan zama acikin shirin ko-ta-kwana a kowane lokaci. Bugu da kari, Gwamnati na shirye-shiryen kafa wasu bataliyan sojoji har guda biyu a yankin kudancin jihar, yayin da sojoji za su ci-gaba da gunadar da harkokinsu na tsaro tare da kakkafa shingayen tsaro a dukkanin wuraren da aka fi samun hare-hare.

Polizei in Nigeria
'Yan sandan masu kwantar da tarzoma a NajeriyaHoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Mai bai wa shugaban kasar shawarwari harwa yau dai ya ci gaba da cewa, shugaban kasa ya umurci hukumar kai agagin gaggawa Nema, da sauran Kungiyoyin kai agajin na musanman irin su Sema da Red Cross wajan gudanar da bincike ga irin bukatocin da wadanda tashe-tashen hankula ya shafa dan kai masu daukin da suke bukata cikin gaggawa. Gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa domin tabbatar da dawowar zaman lafiya a daukacin wannan yanki da ya dade yana matukar fama da rikice-rikicen kabilanci, da siyasa tare da na addinai. Comarade Sunday Tagwai da ke zaman shugaban matasan karamar hukumar Kaura cewa ne ya yi kura ta fara lafawa a daukacin yankin sakamakon irin matakan da hukumomi suka dauka na barbabaza jami'an tsato ta ko'ina.