Yunkurin alkinta al'adu a Najeriya
December 14, 2021Ba dai daukar al'adu da kuma dabi'un da matasa ke yi daga kasashen ketare ne ke janyo barazanar ga al'adun arewacin Najeriyar ba, har ma da batun sauyin da ake samu a fannin zamani da ke shafar tarihi da wasu al'adun kasashe masu tasowa. Wannan dalilin ne ya sanya masu ruwa da tsaki gudanar da wani taro a jihar Kaduna, domin rage bacewar al'adun gargajiyar da wasu tsofaffin kade-kaden taushi na kasar Hausa. Yayin taron na mako guda an tattauna fa'idar da ke tattare da fargar da samari da 'yan mata kan mihinmancin rike al'adunsu, kana aka janyo hankalin hukumomi da kungiyoyi wajen kara ribanya kokarin da suke na rage kalubalen da kananan harsuna ke fuskanta.
Mallam Umar Usman mai Duma shi ne shugaban wata kungiya da ke fafatukar farfado da al'adun gargajiya daga arewacin Najeriya, kuma a cewarsa lallai dai lokaci ya yi na kowa ya bayar da tasa gudunmawar domin rage matsalolin da ke sanya wasu al'adun gargajiya daga arewacin kasar ke neman bacewa a doran kasa. Mahalarta taron da sauran wadanda suka gabatar da kasidu, sun bayyana cewa daukar sababbi da kuma gurbatacciyar tarbiya daga kafafen sadarwa na zamani na daga cikin abubuwan da suke janyo neman bacewar al'adun. Bugu da kari shaye-shaye da yaduwar makamai tare da barkewar rigingimun kabilanci da addinai da rikicin siyasa, na yin mummunan tasiri wajen ruru wutar rigingimu da suka janyo bacewar tarihi da al'adun al'umma a yankin arewacin kasar.