1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NBC ta rufe tashoshin AIT da Ray Power

Uwais Abubakar Idris RGB
June 7, 2019

Rufe gidajen radiyo da Talabijin na Ray Power da AIT  da hukumar NBC ta yi, ya janyo martani mai karfi  tare da ma duba dalilan daukar wannan mataki wanda shi ne karon farko tun bayan kafa mulkin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/3K2D3
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Wannan mataki da hukumar kula da kafofin yada labarai ta Najeriyar ta daauka a kan gidajen radiyo da Talabijin na AIT da Raypower a kasar ya sanya tada jijiyar wuya a kasar, domin an dade rabon da a ga an dauki mataki irin wannan na janye lasisin maimakon gargadi da cin tara da ake yi wa kafofin yada labarai da suka wuce iyaka ko saba ka'ida ta aikin jarida. Matakin da ya biyo bayan dadewa da aka yi ana sa-insa tsakanin hukumar da mai malakar kafofin yada labaran.

Kama dai daga  tsohon mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya zuwa kungiyoyi ‘yan jaridu da ma masu kare hakkin aikin sun mayar da martani mabambanta a kan wannan lamari, da wasu kewa kalon tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro. Tuni dai shugaban gidajen rediyo da talabijin na AIT da Raypower,  Raymond Dokpesi ya bayyana cewa ba za su lamunci lamarin ba.

Dama dai an dade ana kai ruwa rana a tsakanin gidajen rediyo da Talabijin na kamfanin Daar da aka dakatar da lasisin nasa, bisa  zargi na yada bayanai da aka ganin ka iya tunuzura al’ummar Najeriya bisa dalilai na siyasa. Ta kai ga shugaban kamfanin Raymond Dokpesi ya jagoranci zanga-zanga a Abuja. Yanzu dai hukumar gidajen rediyo da Talabijin ta AIT da Raypower sun bayyana shirin daukar matakin kotu a kan wannan dakatarwa.