1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamen masu fafatukar kare dimukuradiyya a Najeriya

Uwais Abubakar Idris MNA
September 30, 2019

Karuwar kame-kamen da jami’an tsaro musamman na farin kaya ke yiwa masu fafutukar kare dimukuradiyya da yakar cin hanci da ma ‘yan jaridu a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3QVvj
Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Daga hankali a kan yawan kamen masu fafutukar a Najeriya da hukumar tsaro ta farin kaya ke yi ya biyo bayan kamen Chido Onumah da suka yi jim kadan bayan saukarsa daga jirgin sama daga kasashen ketare a yanayin da masu fafutuka ke bayyana sabon salo a Najeriya wai kaza ta ji ana shika da dare.

Domin baya ga Chido Onumah da bayan kakaci ta kafofin sada zumunta ya sanya sako shi a daren Lahadia, inda a yanzu ake nunawa juna 'yar yatsa kan cewa ba kama shi suka yi ba. Abdul-Aziz Abdul-Aziz da suke aiki a kungiyar yaki da cin hanci da rashawa musamman a fannin tonon silili da Chido Onumah ya bayyana cewa:

"Borin kunya ya sa suka sake shi, domin kuwa wanda aka dauke shi aka kai sh wani wuri ba inda yake son zuwa ba, ai kama shi aka yi. Abin tashi hankali shi ne yadda ake kama mutane kamar 'yan jaridu ko masu rajin kare hakin jama'a, babban koma baya ne ga tsarin dimukuradiyya."

Har yanzu Omoyele Sowore na tsare duk da oúamranin ba da belinsa da kotu ta yi
Har yanzu Omoyele Sowore na tsare duk da umarnin ba da belinsa da kotu ta yiHoto: CC by M. Nanabhay

Abin da ke tayar da hankali ga masu fafutuka a Najeriya a kan wannan lamari shi ne karuwar kame-kamen a kasar domin baya ga Onumah da ya samu kansa har yanzu akwai Abubakar Idris Dadiyata da tun farkon watan Agusta aka kame shi har yanzu babu labari.

A yayin da wannan ke faruwa rashin mutunta umurnin kotu na zama babbar matsalar a Najeriyar musamman yadda duk da bada belin wasu da ake tsare da su gwamnatin kan kau da kai, na baya baya nan shi ne wanda kotu ta baiwa Omoyele Sowore.

A yayinda ake ci gaba da nuna damuwa a kan wannan lamari, za a sa ido a ga ko wannan zai sanya a samu sauyi daga bangaren gwamnatin da ke bayyana bin doka da oda a kasar.