Kalubalen hafsoshin tsaron Najeriya
January 27, 2021Abin tambayar dai dangane da nadin sababbin hafsoshin tsaron a Najeriya shi ne: su wanene sababbin manyan hafososhin kuma wane kalubale ke gabansu a aikin samar da tsaro a kasar? Sabbin hafsoshin tsaron da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya nada dai, sanannu ne a fagen fama na yaki da ayyukan ta'adanci a kasar, domin kusan dukkansu an dade ana damawa da su a fagen fama, kana sun jima suna rike da manyan mukamai kafin kai wa ga wannan matsayi da yake shi ne kololuwar aikinsu na soja.
Karin Bayani: Ceto 'yan Nijar daga 'yan bindiga a Katsina
Koda yake Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka mai ritaya, masani a fanin tsaro a Najeriyar da ya yi aiki tare da mafi yawan sabbin hafsohin, ya bayyana yadda yake kalon cancanatarsu, sai dai ga Kyaftin Sadeeq Garba Shehu mai ritaya kwarre a fanin tsaron shi ma, ya ce yaki fad an zamba ne.
Shugaba Muhammadu Buharin dai ya nada Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaron kasar sai Manjo Janar Ibrahim Attahir shugaban hafsoshin kasa na kasar. Sauran su ne Real Admiral A Z Gambo shugaban rundunar sojan ruwa sai kuma Air Vice Marshal A.O Amao a matsayin shugaban rundunar sojojin sama. Sun dai kama aiki ne a daidai lokacin da ake doki da murna da ma kosawa da sauyin da ya kai su ga wannan matsayi mafi kololuwa a tsaron Najeriyar, saboda hasashe na samun canji a yadda ake gudanar da yaki da ta'adanci a Najeriyar da ma sauran matsaloli na rashin tsaro a kasar.
Karin Bayani: Majalisun Najeriya sun magantu kan tsaro
Dakta Kole Shettima manazarci a cibiyar dimukurdiyya da ci-gaban kasa da ya fito daga shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar, ya bayyana cewa akwai kalubale a gaban sababbin hafsoshin tsaron Najeriyar. Abin jira cike da fata da shi ne yadda sababbin hafsoshin tsaron za su bai wa marada kunya a kasar, a daidai lokacin da take fuskantar tarin kalubale ta fanin tsaro.