Iska ta haddasa asara a jihar Bauchi
June 19, 2018Talla
Bala'in iskan ya rusa gidajen jama'a da dama yayin da sama da mutane 300 suka jikkata, akalla gidaje 1230 ne suka lalace. Iftila'in dai shi ne irinsa na farko a tarihin jahar.
Tun bayan aukuwar wannan lamarin, gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamiti wadda zai zaga ya kuma duba irin barnar da wannan iska ta yi a cikin garin Bauchi da kewaye. Unguwar Kobi da ke a tsakiyar cikin garin Bauchi ta na daya daga cikin wuraren da wannan masifa ta fi shafa inda shagunan 'yan kasuwa da dama suka ruguje. Tuni gwamnan Jihar Muhammad Abdullahi Abubakar ya mika sakon ta'aziyyar sa ga wadanda wannan masifa ta shafa.