1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hada aure tsakanin masu cutar AIDS

February 22, 2019

Najeriya: Wani matashi a Kaduna ya fito da tsarin hada aure tsakanin masu cutar da ke karya garkuwar jiki wato AIDS.

https://p.dw.com/p/3Dr7w
Uganda Flüchtlingslager in der Nähe von Gulu AIDS Medizin
Hoto: picture-alliance/dpa

Najeriya:  Wani matashi a Jihar Kaduna ya fito da wani tsari na hada aure tsakanin jama'ar da ke dauke da cutar nan da ke karya garkuwar jiki watau AIDS, wanda kawo yanzu masu wannan cutar da dama suka yi auratayya ta dalilin kokarin matashin. Shekaru biyar da suka wuce matashin mai suna Emmanuel Michael ya fara hada masu cutar SIDA aure. A fahimtarsa, kowane dan Adam yana da gudunmawar da zai iya bayar wurin taimaka wa masu dauke da cutar. Domin cimma wannan buri, matashin kan rubuta lambar wayarsa a kan manyan alluna da gine-gine da ke bakin titi, inda ya kan rubuta cewa "duk mai dauke da cutar sida namiji ko mace da ke bukatar auren mai irin wannan ciwo ya tuntunbeshi". Emmanuel Michael ya shaida cewa ko baya ga Jihar Kaduna yana da wakilai a sauran sassa kamar Kano  da Abuja da Enugu da Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.