1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita ga tattalin arizikin Najeriya

January 21, 2021

Bayan share tsawon lokaci cikin halin kunci, Tarayyar Najeriya ta fara tunanin karkata zuwa ga haraji da nufin ceto kasar cikin matsalar rashin kudin da tai wa gwamnati katutu.

https://p.dw.com/p/3oFWJ
Nigeria Präsident Mohammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Duk da kasancewarta kasa mafi karfin tattalin arziki da yawan al'umma, Najeriyar na zaman ta kurar baya a kokarin biyan haraji. Kuma kama daga kamfanonin cikin gida da ma na waje, kaucewa biyan harajin na zaman al'adar da ke da tasirin gaske ga kokarin tara haraji domin hidima ta kasa. Dogaro bisa hajjar man fetur dai, na zaman ta kan gaba cikin hujjojjin watsi da harajin da a baya ke zaman ginshiki na rayuwar  al'umma.

Karin Bayani: Kirismeti cikin larurar corona da rashin kudi

To sai dai kuma faduwar farashin man game da annobar COVID-19, sun tilasta masu mulkin kasar neman sauyin taku da kila karkata zuwa ga harajin domin ayyukan kasar na yau da gobe. Bayan share tsawon sa'o'i ana muhawara, daga dukkan alamu ido yana dada  budewa a bangaren 'yan mulki da ke kallon sababbi na dabarun neman kai wa ga kara biyan haraji a bangaren al'umma.

Nigeria Lagos Stadtansicht
Birnin Lagos cibiyar hada-hdar kasuwanci a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Babajide Sanwaolu na zaman gwamnan jihar Lagos, jiha mafi girma ga batun na haraji a daukacin Najeriyar: "'Yan kasa na da rawar taka wa, haka ita ma gwamnati na da alhakin sauke wa. Dole ne mu yi amfani da dabaru kuma mu daidaita tsakanin tattalin arziki da batun kimmiya. Abun da muke yi yanzu shi ne tattaunawa da mutanenmu. Duk da wahalar da ake fuskanta wajen karba tarte da tattara kudin haraji, muna kokarin ganin mun sauke nauyi gwargwadon hali. Saboda haka abu ne da muke kallo da idanun basira kuma muke nazari da tunani a kansa."

Karin Bayani: Najeriya ta bude karin iyakokin ta da mokobta

Da kyar da gumin goshi ne dai Najeriyar da ke da yawan al'umma kusan miliyan 200, ko bayan tattalin arzikin da ya haura dalar Amirka miliyan dubu 400, ta iya tara Naira triliyan shida da sunan harajin, a yayin kuma da takwararta Afirka ta Kudu da ke bayanta ga batun na tattalin arziki da ma yawan al'ummar, tai nasarar tara kusan Naira triliyan 11 a shekarar da ta shude. Abun kuma da a cewar  Mohammed Nami da ke zaman shugaban hukumar tara harajin Najeriyar, ke da ruwa da tsaki da juyawa harajin baya a bangare na kamfanoni da ragowa 'yan kasuwar kasar. Ko a bana dai kusan kaso 40 cikin 100 na kasafin kudin kasar, na zaman na bashi da gwamnatin kasar ke shirin ci sakamakon faduwar farashin man fetur da Najeriar ke dogaro da shi.