Najeriya: Hanyoyin farfado da tafkin Chadi
February 26, 2018Talla
Zaman taron zai duba hanyoyin kare wannan tafki da ke fuskantar babban koma baya ta sabili da matsalar sauyin yanayi da kuma rikice-rikice. An dai samu halartar wakillai da dama na kasashen da ke kewaye da tafkin na Chadi da suka hada da kasashen Kamaru, Chadi, Nijar, Tarayyar Najeriya, da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda tsawon kwaraki uku mahalarta taron za su dukufa kan hanyoyin sake raya yankunan na Tafkin Chadi kamar yadda hukumar UNESCO ta sanar. Kimanin mutane miliyan 40 ne dai ke dogaro da tafkin na Chadi don samun ruwan sha da sauran ayyukan noma da kiwo. Sai dai sauyin yanayi da wasu matsaloli masu nasaba da rashin kula na kokarin lalata tafkin.