Kogin Zaki tushen arziki a jihar Bauchin Najeriya
May 29, 2018A jihar Bauchin Najeriya kogin Zaki dadadden kogi ne mai matukar tarihi wanda ya yi suna matuka wurin harkar kamun kifi tun shekaru masu yawa. Sai dai kuma yanzu haka baya ga harakokin kamun kifin da aka saba gudanarwa a bakin kogin akwai harkokin kasuwanci daban-daban da jama’a suke gudanarwa a wurin.
Ba jama’ar jihar Bauchi ne kadai suke gudanar da harkokin kasuwancinsu a bakin wannan kogi ba, har da wasu daga kasashe makwafta irin su jamhuriyar Nijer wadanda suma suke baje kolinsu a bakin kogin Zaki. Sana’ar kama kifi ita ce sana’ar da ta fi dadewa ana gudanar da ita a wannan kogi. Kuma har a yau akwai jama’a da dama da suke ci gaba da aiwatar da ita kamar yadda aka sani tun baya.
Sakamakon yadda ake samun tururuwar jama’a a bakin wannan kogi hakan ya sanya wasu matasan teloli bude wata rumfa a gefe inda suke dinki ga jama’a musamman baki da ma wadanda ke da bukata. Jama'a da dama dai na ganin wannan kogi na taimakawa matuka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar ta Bauchi. Sai dai kuma masana tattalin arziki na cewa rashin sanya hannun gwamnatin wurin gyaran bakin kogin da wuraren da ake kasuwancin na iya haddasa komabaya ga cigaban da ake ganin wannan kogi na kawo wa wannan jiha.