1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na neman bashin cike gibin kasafinta

Uwais Abubakar Idris ZMA
September 14, 2021

Shugaba Buhari ya sake neman amincewar majalisar kasar ta bashi iznin karbo bashi na dala biliyan 4 da Euro miliyan 740 daga kasashen waje domin cike gibin kasasfin kudin 2021.

https://p.dw.com/p/40KOV
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Majalisar dokokin Najeriyar da ta koma aiki a Talatar nan bayan hutu na tsawon makwanni, ta bude zamanta ne da wannan batu na bashin da shugaban kasar ya aika mata, wanda kari ne a kan basussukan da ya ciwo daga kasashen waje, lamarin da tun ana shiru ‘yan kasar suka fara nuna damuwa a kan abinda suke hange illa ta bashi ga kasar.

Karin bayani: Shugaba Buhari ya bukaci kwantar da hankula

Ana wa majalisar kallon wacce duk bukatar da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya gabatar mata bata ja. Sanata Abdullahi Adamu dan majalisar dattawan Najeriyar ne da suka karbi wasikar neman bashin. 


"Yan Najeriya dai sukan  kadu da nuna damuwa da zarar sun ji maganar karbo bashin kasashen waje, sanin irin kangi na kunci da ukubar bashi ya haifar masu a shekarun baya, domin sai da ta kai ga yafe wa Najeriyar bashin da ya yi mata katutu daga kungiyar Paris Club na dala bilyan 18 a 2006".

Zauren majalisar wakilan Najeriya
Hoto: Nigeria Office of the House of Representatives


Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya karbo basussuka daga kasashen waje da ya sanya bashin da ake bin Najeriyar a yanzu ya kai Naira triliyan 33, watau dala bilyan 87. Wannan ya nuna bashin ya karu da Naira tirliyan 20, daga lokacin da gwamnatin ta kama mulki a watan Mayun 2015 zuwa yanzu. Amma ga Mallam Abubakar Ali masanin tattalin arziki, ya ce shi bai ga aibu a cin bashi ba amma dole a yi gyara. 

Karin bayani: Kasashen Afirka za su karbo rance
Gwamnatin wamnatin na cewa bata ga abin damuwa ga karbo bashin ba, ministar kula da harkokin kudin kasar Zainab Ahmed, ta ce  bashin da ake ci ba mai daga hankali ba ne. Kwararru na  bayyana cewa gibi na kasafin kudin da Najeriyar ke son ta cike da wannan bashi dai na nuna yanayi da tattalin arzikin kasar ya shiga.