1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyi a kan dokar aikin jarida a Najeriya

July 12, 2021

A Najeriya kafafen yada labarai sun fara wani shiri na yin bore ga kokari na yin kwaskwarima a bisa dokokin aikin na jarida.

https://p.dw.com/p/3wNip
Afrika Nigeria Zeitungsverkauf Presse
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Daya bayan daya dai manyana jaridun tarrayar Najeriya suka ware shafin farko na jaridun Litinin(12-07-21) domin nuna hatsarin da kasar take ciki ga makomar 'yancin labarai. Kamfen din da hadin gwiwar kungiyoyin 'yan jarida, da editoci da kuma masu jaridu na kasar suka dau nauyi dai na cewar kwaskwarimar da majalisar wakilai ta kasar ke neman yi ga dokokin aikin na jarida guda biyu dai na da biyu. Gamin gambizar ta masu ruwa da tsaki da jaridar dai sun ce abun da ke shiri ya faru a majlisun na da burin toshe damar labarai ga daukacin al'ummar tarrayar Najeriyar. Sabon kamfen din na zaman na baya-baya a kokari na masu jaridar na dauka ta hankalin daukacin kasar bisa rikicin da ya faro daga wani kudurin dokar da wani dan majalisar wakilar daga Oyo ya gabatar, amma kuma masu jaridar ke masa kallon da hannu na gwamnatin. 

An dai dauki lokaci ana muhawara cikin tarrayar Najeriya bisa makomar aikin da ya kalli karuwar bazuwar labaran karya da kila kokarin bacin suna ga 'yan kasar a cikin sunan 'yancin na jarida. Kuma wannan ne karo na biyu cikin tsawon kasa da shekaru guda biyu da majalisun tarrayar Najeriyar ke yunkurin rage shiga dawa ta masu jaridar da ake zargi da fakewa a cikin kundin tsarin mulki na kasar da nufin tafka ta'asar da ke barazanar raba kai da kila jefa makoma ta kasar a cikin mummunan hali. Babban kalubalen da ke gaba na masu jaridar tarrayar Najeriyar dai na zaman iya tsarkake aikin da nufin samun gyara, ko kuma tilasta gyaran kansu daga mahukuntan da ke kallon ta yi baki ta kuma lalace.