Najeriya: Buhari zai je London don duba lafiyarsa
May 8, 2018Talla
Buhari mai shekaru 75 bai yi karin bayani kan lafiyar ta sa ba. Sai dai ba wannan ne karon farko da yake zuwa birnin London kan batun lafiya ba, don kuwa a bara ma ya shafe fiye da wata guda ya na jinya a wani asibitin kasar Britaniyan kan cutar da ba a baiyana wa jama'a ba.
Tuni masu sharhi suka soma tsokaci da cewa, wannan batu ka iya haifar da damuwa kan koshin lafiyar shugaban da ke da niyyar sake tsayawa takara a babban zabe na shekarar 2019.