Rashin biyan 'yan sanda alawus a Maiduguri
July 4, 2018Bayan da a ranar Talata fadar gwamnatin tarayyar Najeriya ta gayyaci sifeto janar na 'yan sandan kasar domin jin bahasi kan zanga-zangar da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka yi a Maiduguri, hedkwatar 'yan sandan Najeriya ta tura wani kwamiti na musamman domin yin binciken musabbabin rashin biyan 'yan sanda da aka tura aiki tabbatar da tsaro, alawus-alawus dinsu.
Daga farko dai hedkwatar 'yan sandan ta musanta cewa jami'anta sun yi zanga-zanga a garin na Maiduguri, don neman a biya su hakkokinsu, inda ta ce 'yan sandan sun je neman bayanai ne kan tsaiko da aka samu na biyan kudade alawus-alawus.
An yi amai an lashe
To sai bayan da manema labarai suka fitar da asalin labarin, wanda ya nuna 'yan sandan na zanga-zanga, fadar gwamnatin Najeriya ta gayyaci sifeto janar na 'yan sanda domin jin bahasin abin da ke faruwa wanda bisa wannan ne hedkwatar 'yan sandan ta yi gaggawar tura kwamitin na manyan kusoshin rundunar don shawo kan matsalar.
Kwamitin wanda ya kunshi babban mataimakin sifeto janar na 'yan sanda da kuma wasu manyan jami'an 'yan sanda sun isa Maiduguri domin neman bakin zaren magance matsalar.
Wata majiya ta 'yan sandan ta tabbatar da cewa da zuwan kwamitin har ya gana da shugabannin 'yan sanda da ke Maiduguri, kuma an tabbatar da cewa za a yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an biya wadannan bayin Allah kudadensu nan bada dadewa ba.
Barazanar sake yin zanga-zanga
Wani dan sanda da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar da hakan ta wayar tarho, ya jaddada barazanar da suke yi ta in ba a biya su nan da karshen makon nan ba, za su sake yin zanga-zangar da ta fi wacce suka yi a baya.
Ban da kudaden alawus-alawus da ba a biya su, 'yan sanda sun kuma yi zargin cewa ba su da wajen kwana, inda da dama daga cikinsu ke kwana a gaban ofisoshin da ke harabar hedkwatar 'yan sanda.
Masana da masharhanta sun bayyana fargabar cewa rashin biyan 'yan sandan hakkokinsu wata barazana ce ga kokarin wanzar da zaman lafiya a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, wacce ta shafe kusan shekaru goma tana fama da rikicin Boko Haram.
Talakawan shiyyar sun bayyana yanayin da cewa abin tsoro ne kuma ya kamata hukumomi su yi dukkanin mai yiwuwa wajen biyan hakkokin jami'an tsaro da kuma magance sake aukuwar jinkirin biyansu.
Rashin magance wannan matsalar ko kasa hukunta wadanda suka haifar da jinkirin biyan hakkokin 'yan sandan ka iya zama kalubale ga daukacin kokarin da gwamnati ke yi a yaki da cin hanci kamar yadda masu fashin baki ke cewa.