1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Garkuwa da 'yan makaranta 333

Abdourahamane Hassane LMJ
December 16, 2020

Har yanzu iyayen yaran da aka sace a makarantar Kankara da ke Jihar Katsina Najeriya na cigaba da dakon mahukuntan kasar su ceto musu ya'yan su daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/3mo9t
[No title]

Kawo yanzu dai dalibai 333 ne ake nema wadanda 'yan bindigar suka sace tun a ranar Asabar 12 ga wannan wata na Disamba da muke ciki. Lamarin dai ya jefa al'umma cikin firgici ganin wannan shi ne karon farko da aka kai irin wannan hari a makaranta a yankin Arewa maso Yammacin kasar da ashi ma ya bi sawun takwaransa na Arewa maso Gabashin Najeriyar a fannin hare-haren Ta'addanci.

Da farko dai 'yan bindiga ne suka yi ikirarin sace yaran, amma kuma daga bisani kungiyar Boko Haram da ta kafa tungarta a yankin Arewa maso gabashin kasar, ta ce ita ce ke da alhakin dauke daliban.

Wannan matsala dai, ta sanya rufe daukacin makarantun a jihar ta Katsina da ma wasu jihohin yankin Arewa maso Yamman, a wani mataki mai kama da na idan gemun dan uwanka ya kama da wuta.