Kotu ta yi watsi da karar Atiku kan zabe
October 30, 2019A Najeriya, kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta PDP ta daukaka a gabanta, tana mai kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 watan Febuwarin da ya gabata, wanda dan takarar jam'iyyar APC Muhammadu Buhari ya lashe da kaso 56 daga cikin dari a yayin da abokin hamayyar tasa Atiku Abubakar ya samu kaso 41 daga cikin dari.
Babban alkalin kotun Tanko Muhammad ne ya bayyana wannan hukunci a wannan Laraba inda ya ce, sun yi watsi da karar ne domin kuwa zarge-zargen da hujjojin da jam'iyyar adawar ta gabatar ba su gamsar da kotun ba. Amma ya ce sai a nan gaba ne kotun za ta bayyana dalillan da suka sa illahirin alkalai bakwai na kotun suka yi watsi da karar jam'iyyar adawar.
Dama dai a tsakiyar watan Satumban da ya gabata, a matakin farko na shari'a, kotu ta yi watsi da karar da dan takararar adawar Atiku Abubakar ya shigar a gabanta domin neman a soke sakamakon zaben. Da wannan hukunci dai, kotun ta kawo karshen rikicin sakamakon zaben wanda aka share watanni takwas ana yi tsakanin manyan jam'iyyu biyu na Najeriyar a gaban kuliya.