1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: APC na cikin rudani kan mataimakin Tinubu

Ubale Musa M: Ahiwa
June 17, 2022

'Yan sa'o'i kafin cikar wa'adin hukumar zabe na mika sunayen masu takara, jam'iyyar APC a Najeriya ta bar miliyoyi na ‘yan kasar cikin duhu bisa muhimmin zabe na 2023.

https://p.dw.com/p/4CsQO
Shugaba Buhari da shugaban APC lokacin tabbatar Bola Tinubu a matsayin dan takaraHoto: Nigeria Prasidential Villa

Ya zuwa tsakar daren ranar Juma'ar nan ne dai wa'adin hukumar zaben Najeriya ta INEC ke cika game da mika sunayen masu takara ta shugaban kasa da mataimakansu ga hukumar. To sai dai kuma har ya zuwa yammacin Juma'ar dai jam'iyyar APC mai mulki na ci gaba da zama cikin karatun kurma bisa ko wane ne ke tabbas zai tsaya mata takarar mataimaki na shugaban kasar a zaben na badi.

Babu dai sanarwa walau daga hedikwatar jam'iyyar ko kuma ofishin yakin neman zabe na dantakararta, balle kuma fadar gwamnatin kasar game da zaben da al'umma tarrayar Najeriyar ke zaman jira a halin yanzu. To sai dai kuma majiyoyin fadar gwamnatin kasar sun tabbatar da aike sunan Ibrahim Kabir Masari domin zama dan takarar riko na mukamin mataimakin da ya dauki lokaci yana jawo dagun hakarkari ciki dama wajen jam'iyyar.

Nigeria, Abuja, Muhammadu Buhari, Gouverneur, Bola Ahmed Tinubu, Politik, Krise, Politika, Wahl, 2023,
Shugaba Muhammadu Buhari da Bola Tinubu suna ganawaHoto: Official-State House Abuja Nigeria

Masarin da ya fito daga Katsina a sashen arewacin kasar dai na zaman tsohon jami'i na walwala a jam'iyyar APC na kasa, kuma daya a cikin na hannun dama a siyasar Bola Ahmed Tinubu tun bayan gamayyar da ta kai ga haihuwar APC. To sai dai kuma ba shi da wata kwarewa ta mukami walau a bangaren zartarwa ko kuma yin doka cikin fage na siyasar Najeriyar da ke da tsidau da kaya.

APC dai kuma a fadar Barrister Isma'il Ahmed, daya a cikin makusantan Bola Tinubu na da har ya zuwa watan Augustan da ke tafe na sauya sunan dan takarar mataimaki na shugaban kasar in ta kama. Duk da cewar dai masu tsintsiyar sun yi nasara ta fitowa daga zaben fidda gwanin cikin dauri guda daya, har ya zuwa yanzu kai na rabe bisa addinin mataimakin.

A yayin da alal ga misali fadar gwamnatin kasar ke kallon yiwuwar fitar da Kirista domin daidaiton addini, dan Tinubun na hangen fitar da Musulmi da nufin samun goyon bayan miliyoyin 'yan zaben arewacin kasar da ke iya sauya da dama.