1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci ga tsohon gwamnan Taraban Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 30, 2018

Babbar kotu da ke Abuja fadar gwamnatin Najeriya, ta yanke hukuncin daurin shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba ga tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame.

https://p.dw.com/p/2yfok
Karte Map Nigeria Taraba ENG
Hoto: DW

Mai shari'a Adebukola Banjoko ya ce kotu ta samu tsohon gwamnan na jihar Taraba da ya yi mulki tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 da laifuka 27 daga cikin 41 da aka tuhume shi da su, sakamakon karkatar da kudi sama da Naira bilyan guda a lokacin da ya ke kan karagar mulki. Wakilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris ya ruwaito cewa, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ce ta kai shi kara a kan wannan laifi, inda kotun ta kwashe fiye da sao'i hudu kafin ta yanke masa hukuncin. Hukuncin na zama daya daga cikin na baya-baya nan da hukumar EFCC ta samu nasara a kotunan Najeriya.