1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An sanya dokar hana fita a Kaduna

October 17, 2016

Dokar hana zirga-zirga tsawon sa'o'i 24 saboda sabon tashin hankalin da ya barke a kudancin Kaduna.

https://p.dw.com/p/2RJmF
Nigeria - Kadnuna
Hoto: Getty Images

Sabon Tashin hankalin da ya barke a garin Godo-godo na karamar hukumar Jama'a da ke kudancin jihar Kaduna ya janyo asarar rayukan mutane 20, da barnata miliyoyin dukiya, lamarin da sanya gwamnati kafa dokar ta-baci da hana zirga-zirga tsawon sa'o'i 24 a dukkanin kawayen garin.

Gwamnatin jahar kaduna ta yi tur da sabon tashin hankalin.

Kamar yadda wakilinmun na Kaduna Ibrahima Yakubu ya ruwaito, tuni mataimakin Gwamnan jihar Achtech Bala Barnabas Bantex, ya bukaci al'ummar kudancin Kaduna da su kwantar da hankalinsu, su kuma bi doka da oda, tare da kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta hukunta duk wanda aka samu da hannu dumu-dumu wajan tayar da zaune tsaye.

Tun da farko da yake sanar da dokar hana zirga-zirgar, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Dr Bege Katuka ya shawarci daukacin jama'ar yankin da su kasance masu zaman lafiya da kuma bin dokokin da gwamnati ta shinfida na tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Dr Bege ya tabbatar da cewa an girke jami'an tsaro domin shawo kan dukkanin wasu matsalolin da ke addabar daukacin yankin na Kudancin Kaduna

Wannan Rikicin dai ya auku ne yayin da wasu matasan gari suka tare wasu motoci da suka banka masu wuta tare da mutane a cikinsu, lamarin da ya tayar da hankalin daukacin kauyukan yankin.