1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage shirin rigakafin corona a Najeriya

January 22, 2021

A wani abun da ke zaman ta leko tana shirin komawa ga fatan Najeriya na samun rigakafin annobar COVID-19 cikin watan Janairun da ke shirin karewa, gwamnatin kasar ta ce ta dage shirin har sai watan Fabrairu.

https://p.dw.com/p/3oI6C
Impfstoff Pfizer-BioNTech COVID-19
Karancin allurar rigakafin coronavirus a kasashe masu tasowaHoto: Christof STACHE/AFP

A baya dai Najereiyar ta ce za samu allurar rikagafin kimanin miliyan 10 a wannan wata na Janairu da muke ciki. Kuma tuni kasar ta ce ta fara shiri, tare da samar da cibiyoyin ajiyar rigakafin BioNTech dubu 100, baya ga dubban miliyoyi da kasar ta ce ta ware da nufin aikin rigakafin.

Karin Bayani: Matsalar rashin zuwa gwajin corona a Najeriya

To sai dai kuma babu zato ba tsamanni masu mulkin na Abuja sun ce allurar rigakafin tana shirin kai wa har ya zuwa watan gobe na Fabarairu. Kuma ko a watan goben maimakon miliyan 10 dai, Najeriyar za ta karbi abun da bai wuce kwaya dubu 100 na allurar rigakafin kamfanin na BioNTech-Pfizer, adadin kuma da ba zai isa ko da kaso daya a cikin 100 na al'ummar kasar ba.

Deutschland Berlin | Coronavirus, Impfzentrum
Yayin da aka yi nisa wajen yin allurar rigakafin a wasu kasashe, an bar kasashe irin Najeriya a bayaHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Wani taron majalisar tattalin arzikin kasar na gwamnoni da aka gudanar a ranar Alhamis dai, ya ce akwai sauran tafiya kafin iya kai wa ga tabbatar da samun allurar rigakafin coronan da a yanzu kasashen duniya ke wasoso. Gwamnatin kasar dai ta ware Naira miliyan dubu 10 da nufin gina wata sabuwar masana'antar yin allurar da zarar kasar ta kai ga iya samun dama daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Karin Bayani: Kirismeti cikin larurar corona da rashin kudi a Najeriya

A cewar jagoran yaki da COVID-19 a cikin Najeriyar Boss Mustapha tunkarar annobar zai yi nasara ne tare da batu na kulawar al'umma ko bayan batun na rigakafin allurar ta kariya. Tarayyar Najeriyar dai na fuskantar ta'azarar  corona da ya zuwa yanzu adadin yawan wadanda suka kamu da ita ya haura dubu 116. Sai dai kuma a fadar Dakta Ibrahim Kana da ke zaman daraktan ma'aikata lafiyar kasar,  Abujar ta tashi tsaye da nufin kula da masu dauke da cutar a matakai dabam-dabam. Najeriyar dai na bukatar Naira miliyan dubu 400, kafin iya kai wa ga bayar da kariya  ga 'yan kasar sama da miliyan 200.