1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Siyasa za ta iya tafiya da addini ?

March 15, 2022

A Najeriyar ra'ayi na rabe bisa matakin wata darikar cocin da ta ce ta kafa sashe na siyasa domin taka rawa a zabukan da ke tafe abin da wasu suke ganin daidai wasu kuma na ganin bai dace ba.

https://p.dw.com/p/48WVq
National Assembly in Abuja, Nigeria
Hoto: DW

Darikar RCCG din dai na zaman daya a cikin manya na darikun addinin na Kirista da ke da ya'yanta cikin manyan jam'iyyun kasar dabam dabam. Kuma ba ta boye burinta na tsomin baki da kafa cikin fagen siyasa ta kasar da ke dada daukar zafi yanzu. Duk da cewar dai ba yana zaman sabon abu ba hawa na munbari a bangare na malaman addinin da nufin nunin taka rawa a fagen siyasar, wannan ne karo na farkon fari da wata darikar addinin ta fito fili domin bayyana aniyar kallo na siyasar da idanu na basira. Matakin RCCG dai na nuna alamar sabon tsari na siyasa da kasar ke shirin dauka a nan gaba.

Rarrabuwar kawunan al'umma a kan hada addinin da siyasar

Christliche Kirche und im Hintergrund Moschee in Abuja, Nigeria
Hoto: Katrin Gänsler

A baya dai rabuwar kan da ke cikin addinin ta kai da tada babbar kura a cikin Najeriyar in da siyasa da batun addinin ke neman su cakude a harkoki na kasar. Reverend Sunday Ibrahim dai na zaman sakataren kungiyar Kiristocin Najeriyar ta CAN reshen arewacin kasar da kuma ya ce RCCG ta cancanci yabo cikin fagen siyasar Najeriyar a halin yanzu: ''Ni ina ga abun da kowace Ikilisiyya ta yi ne abun da kowace coci ya kamata ta yi ne. domin ko gida ne ya kamata akwai siyasa, ko a makarantu akwai siyasa.Ya kamata su zama ido ga mutanensu.Yaro na tashi da faduwa in yana rarrafe har ya tashi. Zai iya zama an yi kuskure amma da kadan-kadan abubuwa za su yi tafiya yadda ya kamata.

Rawar addinin a cikin harkoki siyasar a tsakanin manya na malaman addinai na kasar 

Moschee in Abuja
Hoto: picture-alliance/ dpa

Kokarin jan kare zuwa ga mashaya ko kuma wuce makadi cikin rawa dai daga dukkan alamu ra'ayi yana shirin zama daya bisa rawar addinin a cikin harkoki na siyasar a tsakanin manya na malaman addinai na kasar. Kuma kafa sashe na siyasar a cikin darikar RCCG a fadar Ustaz Hussaini Zakaria da ke zaman wani malamain addinin Musulunci na iya kai wa ya zuwa  bude idanu na Musulmi na kasar bisa sabon na'uin na siyasa.'' mataimakin shugaban kasa a Najeriya a yau malamin addini ne, yana da coci da yawa a kasar nan kuma wannan darika ta RCCG tasa ce. Kuma ita ta bayyana burin da take shirin aiwatarwa na fadikar da ya'yanta zuwa su zabi Kirista don shi ne ya fi amana da gaskiya. Don haka yanzu suma Musulmi sai su yi koyi da wannan su dauko wani Malami ko wani Limami ko wani Sheik da zai iya rike amana mu ce masa bisimillah. Mu tashi daga 'yan amshin shata kamar yadda wannan gwamnatin ta yi wa malamai. Suka tura motar, ta tashi ta buda musu kura da tabo, ta tafi ta bar su''

Ko ma ya take shirin kayawa a tsakanin manyan addinan da ke fadin sai nasu ko kafar katako dai, Najeriyar dai na da babban darasi daga Lebanon inda siyasar ke hade da batun addini amma kuma kasar ke cikin wani mawuyacin hali.