Harin mayakan Houthi kan fararen hula
November 1, 2021Mutum sama da ashirin ne suka rasa rayukansu a sakamakon wasu jerin hare-hare da ake zargin mayakan Houthi da kai wa, kan wani masallaci da kuma wata makarantar Islamiyya, hare-haren sun rutsa da fararen hula, ciki har da mata da kananan yara, sun kuma raunata wasu da dama a yayin da ake fargabar karuwar alkaluman mamatan saboda tsananin da wadanda suka ji raunin ke ciki.
Kawo yanzu dai, babu wanda ya dauki alhakin kai harin da gwamnatin kasar ta ce na ta'addanci ne amma ta dora alhakin harin kan mayakan na Houthi. Tun bayan barkewar rikici a tsakanin mayakan da ke adawa da gwamnatin Yemen, shekaru sama da bakwai da suka gabata, mutum sama da dubu dari suka rasa rayukansu inda miliyoyin 'yan kasar suka shiga cikin yanayi na tsananin bukatar taimako.