Yuganda: Mutum 16 sun mutu a rikicin siyasa
November 20, 2020Mutum goma sha shida ne yanzu aka tabbatar sun mutu a rikicin da ya biyo bayan kama dan takarar shugaban kasar Yugandan nan Bobi Wine. Rahotanni na cewa, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai saka kwalla da harsashen roba a tarwatsa dandanzon masu zanga-zangar da ke nuna adawa da kama Mista Wine da aka yi. A Kampala babban birnin kasar, masu zanga-zangar sun yi ta kone-kone da toshe manyan tituna tare da fasa shaguna suna wawashe kayayyakin ciki.
Bobi Wine dai, asalin sunansa Robert Kyagulanyi mai shekaru 38 da haihuwa, ya kasance babban abokin hamayyar Shugaba Yoweri Museveni a zaben. Ya sha alwashin ceto kasar daga cikin kangin talauci da rashin aikin yi a tsakanin matasa, fitaccen mawakin yana ci gaba da samun goyon bayan matasa da ke ganin shi zai iya cire musu kitse a wuta.
Majalisar Dinkin Duniya da Amirka na daga cikin wadanda suka nemi a saki Bobi Wine tun bayan kama shi da aka yi a ranar Larabar da ta gabata. Hargitsin na zuwa ne makonni biyu kafin gudanar da zaben Shugaban kasar, da fitaccen mawakin ke sahun gaba a fafatawa da Shugaba mai ci Yoweri Museveni.