Mutanen da suka mutu a Chemnitz sun karu
August 28, 2018Talla
Rundunar 'yan sandan Jamus ta bayyana yawan mutanen da suka jikkata a zanga-zangar kin jinin baki a garin Chemnitz na gabashin kasar daga mutane shida zuwa 20. Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Talatar, rundunar ta ce 'yan sanda biyu, da masu akidar kyamar baki da masu zanga-zanga tara sun ji rauni a cikin rikicin.
Ministar shari'a ta Jamus Katharina Barley ta yi kira ga hukumomin Jihar Saxon da ke gabashin kasar da su c gaba da gurfanar da masu akidar kyamar baki da suka aikata laifukan a tashin hankalin da ya barke a garin Chemnitz. Tuni dai Jamusawa suka fara nuna fargaba dangane salon da zanga-zangar ke dauka.
Mutuwar wani dan shekaru 35, wanda ake zargi wani da ke da tushe da Siriya da Iraki ne ta haddasa wannan tashin hankalin.