1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanar da sunayen wadanda suka lashe kyautar Nobel ta bana

October 5, 2020

Michael Houghton da Hervey J. Alter da kuma Charles M. Rice su ne mutanen da aka bayyana a matsayin wadanda suka lashe kyautar Nobel ta wannan shekara ta 2020.

https://p.dw.com/p/3jSOt
Infografik Nobelpreis Medizin Verteilung Frauen Männer 1901-2020 EN

Michael Houghton dan kasar Birtaniya da kuma Hervey J. Alter da Charles M. Rice su ne aka bayyana a ranar Litinin din nan, a matsayin wadanda suka lashe kyautar Nobel ta bana a harkar lafiya. Nasarar da mutanen uku suka samu, ta biyo bayan binciken da suka gudanar da kuma ya yi sanadiyyar gano cutar ciwon hanta mai rukunin C tun a shekarun 1970 zuwa 1980.

Binciken a cewar kwamitin tantance wanda ya lashe kyautar ya taimaka matuka, wajen samun maganin nau'in cutar ta hanta a fadin duniya da ta hallaka mutane da dama, hakan kuma ya kara kyautata kiwon lafiyar al'umma.

Gano nau'in cutar ta hanta mai rukuni C ya biyo bayan wanda aka taba yi na rukunnan A da B wadanda suma ke mummunar illa ga lafiyar bil adama.

Kiyasin hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, WHO, na nuni da cewa kimanin mutane dubu 70 ke kamuwa da cutar a duk shekara inda kuma wasu dubu 400 ke rasa rayukkansu.