Mutane tara sun mutu a faɗan ƙabilanci a Bauchi
January 22, 2012Aƙalla mutane tara sun rasa rayukansu a Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, yayin da wasu mutane 12 suka jikata, lokacin wani harin da aka kai wa kirostocin wannan ƙaramar hukumar ta arewacin tarayyar najeriya. Wani mai magana da yawun ƙabilar sayawa mai suna Bukata Zhyada ya bayyana wa kanfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa ɓabilar hausa fulani ne suka afka musu da faɗa da daren asabar zuwa lahadi. Wannan rikicin ya zo ne a daidai lokacin da wasu bama-bamai suka fashe a wurare biyu a cikin birnin Bauchi, ba tare da jikata ko da mutum guda ba.
Harin na Bauchi ya fara a daidai lokacin da hukumomin kano suka sassauta dokar da suka kafa daga ta hana yawo i zuwa ta hanna fitar dare, bayan da aka samu lafawar al'amura a jihar da ta yi fice a fannin kasuwanci. A halin yanzu dai jami'an tsaro na ci gaba da sintiri akn manyan titunan cikin birni inda wasu jerin hare-hare suka hadassa salwatar rayukan mutane da dama. Hukumomin lafiya sun nunar da cewa ya zuwa yanzu mutane 178 ne suka rasa rayukansu a jerin hare-haren bama-bamai da ƙungiyar Boko haram ta ɗauki alhakkinsu.
Mawallafi Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu