Murna tare da kyakkyawan fata sun barke a Gambiya
Bayan shekaru 22 na kama-karya, a wannan Asabar 'yan kasar Gambiya sun yi bikin kaddamar da sabon Shugaban kasa Adama Barrow. Akwai manyan kalubale a gaban Barrow.
Bude sabon babi a Gambiya
Adama Barrow ya lashe zaben demokradiyya na farko cikin shekaru gommai a Gambiya. A ranar Asabar 18 ga watan Fabrairu aka yi bikin rantsar da shi a hukumance. Da farko tsohon shugaba Yahya Jammeh ya so ya ki sauka, ga kuma halin rashin tabbas a Gambiya, shi ya sa aka rantsar da Barrow a makociyar kasa Senegal. An tsaurara matakan tsaro saboda bikin.
Kade-kade da wakoki sun burge mutane
A yayin bikin rantsar da Adama Barrow, mawakan zamani kamar a nan wata mwakiyar kasar, sun shiga jerin wadanda suka burge jama'a mahalarta bikin da ya gudana a filin wasa na 'yanci da ke Bakau a kasar ta Gambiya.
Gambiya ta yanke shawara
A birnin Serrakunda da ke zama mafi girma a Gambiya, shirye-shiryen bikin ya kankama ba kama hannun yaro. Da taken #GambiaHasDecided - wato Gambiya ta yanke shawara - an bayyana a fili, bayan hukuncin da mafi yawan 'yan Gambiya suka yanke a zaben da suka yi na neman canjin siyasa da tattalin arziki. Yanzu taken na kan rigunan T-Shirt da dama.
Cincirindon jama'a
Dubun dubatan mutane aka sa rai za su halarci bukukuwan a dandalin wasa na 'yancin kai. Kasancewa dandalin zai iya daukar mutane dubu 30 kadai, an kakkafa wuraren zama na karfe tare da samar da manyan akwatunan telebijin da za a iya kallon bikin da ke gudana kai tsaye daga filin wasan.
Fatan samun bunkasar tattalin arziki
Kasuwar Serrakunda daya ce a cikin manyan wuraren cinikaiya a kasar. Muhimman ababan da ke sama wa kasar kudin musaya su ne gyada da harkar yawon bude ido. Gambiya na daga cikin kasashen duniya da suka fi talauci. A saboda rashin tabbas bayan zabe, 'yan yawon bude ido sun kaurace wa Gambiya, abinda ya kara kassara tattalin arzikin kasar.
Kyakkyawar zamantakewar al'umma
A kasar da mafi yawan al'ummarta Musulmi ne, akwai Kiristoci da dama. Gambiya ta yi suna saboda kyakkyawan zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da masu al'adu mabambamta. Sai dai a shekarun da suka wuce mahukuntan kasar sun yi ta jaddada bambamcin da ke akwai tsakanin kabilun kasar da mabiya addinai dabam-dabam, abin da ya janyo zaman dar-dar. 'Yan kasar na fatan bude sabon babi.
Babban fata
'Yan Gambiya da yawa na hangen kyakkyawar makoma ga rayuwarsu, duk da tarin matsalolin da ke kasar: tattalin arzikinta ya fadi kasa warwas, ba kudi a baitul-malin gwamnati, ga karancin hasken wutar lantarki. Adama Barrow ya yi wa 'yan Gambiya alkawura da dama, yanzu suna sa rai sabuwar gwamnati za ta cika alkawuran kawo canji da ta yi.