1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kan sha'anin tsaro karo na 58

Abdourahamane Hassane LMJ
February 21, 2022

An kammala taron tsaro da aka yi a birnin Munich na Jamus, inda aka tattauna bututuwa da suka shafi rikice-rikice da ake fuskanta a duniya da samar da hanyoyin zaman lafiya mai dorewa.

https://p.dw.com/p/47NNQ
Taro kan tsaro a Munich I 2022
Taro kan tsaro a birnin Munich na Jamus ya tabo batutuwa da dama a banaHoto: Matt Dunham/Getty Images

An dai kammala taron kan sha'anin tsaro na birnin Munich karo na 58 cikin wani yanayi da hankalin shugabannin kasashen duniyar da suka halarci taro su kusan 35 ya karkata a kan batun Ukraine, daf da lokacin da ake yin hasahen cewar Rasha za ta kai mamaye Ukraine din. Ministar tsaron Jamus Christine Lambrecht ta sake yin watsi da bukatar da Ukraine ta gabatar ga taron Munich, na samun makamai. Shugabannin sun yi dogon nazari a kan  batun take hakkin dan Adam a Chaina da kara karfafuwar hulda tsakanin Amirka da Turai da shirin nukiliya na Iran wanda har yanzu ake yin takaddama a kansa.

Ostiriya  | Tattaunawa kan makamashin nukiliyar Iran
Kasashen Yamma, na ci gaba da tattaunawa da Iran kan makamashin nukiliyartaHoto: EU Delegation in Vienna/Handout/AFP

Sai dai a hannu guda Isra'ila ta nuna damuwarta kan cewar duk da shirin yarjejeniyar nukiliyar da Iran za ta kulla da kasashen duniya, ya kamata hukumar kula da nukiliya ta duniya ta ci gaba da bincikarta domin sanin ko ta boye wasu cibiyoyin. Wani abin da ya dauki hankalin taron shi ne fargabar sake barkewar yaki a Bosniya, wanda bayan yakin da aka yi a shekara ta 1990 da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin dubu 100 kafin NATO ta shiga tsakanin a cimma yarjejeniya a Dayton kan raba kasar biyu. A yanzu an fara samun rashin jituwa tsakanin kasashen makobtan juna. Josep Borrell jagoran diplomasiyya na EU kan harkokin waje da manufofin tsaro ya ce, ba za su taba amicewa da sake tarwatsewar kasashen na Bosniya da Sabiya ba. Kwararru a karshen taron sun yi amannar cewa, sai an kara zage damtse a kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya sakamakon yadda yake-yake da rigingimu ke karuwa a duniya.