Mundari: Kabilar da ta yi nisa da rikicin Sudan ta Kudu
'Yan kabilar Mundari na zaune a wani yanki da ke da nisan tafiyar sa'o'i hudu daga Juba babban birnin Sudan ta Kudu. Kiwon shanu shi ne abin da mutanen suka fi raja'a a kai. A lokacin sanyi su kan kauracewa yankin nasu.
Wajen yin kiwo a lokacin sanyi
'Yan kabilar Mundari ke nan da shanunsu, inda suke yin kiwo a wani yanki da ba shi da tazara sosai da garin Terekeka. Mutanen kan zo nan ne domin nemawa shanunsu abinci. Dole ne shanun su ketara kogin Nilu domin isowa nan, wanda hakan kan tayar da hankalinsu saboda gudun yin asarar dabbobinsu.
Muhimmancin shanu ga 'yan Mundari
A kowacce safiya, a kan shafawa shanun toka domin kawar da kwari da kaska da ka iya yi musu illa. Baya ga haka ana goge kahon don ya yi sheki. Shanu na da mutakar muhimmanci ga 'yan kabilar Mundari, domin idan mutum ba shi da su, ba zai iya aure ko kasuwanci ko kula da iyali da sama musu abinci ba.
Alakar Mundari da Larabawa
A lokacin da suke hutawa, 'yan kabilar Mundari kan sha irin tabar nan ta Shisha, wanda hakan ke nuna rin alakarsu da Larabawa. A shekara ta 2011 ne kasar Sudan ta rabu gida biyu. 'Yan Mundari sun shafe tsawon lokaci suna rikici da Arewa da kan gujewa shari'ar Musulumci da gwamnatin Khartoum ke amfani da ita.
Zane irin na gado
Irin zanen gado da 'yan Mundari kan yi a goshinsu na nuna cewar mutum ya kawo karfi. Ana kuma iya amfani da zanen wajen gane inda mutum ya fito, sannan matsafa kan ce zanen na nuni da hukuncin kisa da aka yankewa wani. Ana amfani ne da wuka wajen yin irin wannan zanen, amma kuma hakan na kara hadarin kamuwa da cutar HIV/AIDS ko kuma SIDA.
Zaman lafiya ya haifar da tsadar aure
Yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Salva Kiir da abokan hamayyarsa suka amince da ita, na nufin za a janye sojoji daga yankuna da dama. Hakan ya sanya matasa da yawa sun shiga neman matan da za su aura. Hakan ya sa sadaki ya kara tsada, inda yanzu ake bayar da shanu 40 maimakon 20.
Dawowar 'yan gudun hijira
Paul dan gudun hijira ne da ya koma kauyen, bayan da ya shafe shekaru tara a sansanin 'yan gudun hijira na Kukuma da ke kasar Kenya. Matashin na son komawa makaranta domin ci gaba da karatunsa, sai dai wata kungiyar farar hula na son ganin ya biya dala 50 a kowacce shekara. Wannan kudi ya yi wa mahaifinsa yawa matuka.
Busa kaho wajen kiran shanu
Nan wani dan Mundari ne yake busa kaho domin kiran shanunsa. Karar busar yana kaiwa wurare masu nisa. Wannan abu kan kasance mai hadari, domin ya kan haifar da rikici tsakanin 'yan Mundari da 'yan kabilar Dinka. A lokuta da dama a kan kwashe shanunsu a kadasu babban birnin kasar domin sayar da su, kuma mutane masu dauke da manyan bindigogi ne kan yi hakan.
Fata na samun sauyin rayuwa
Matasan Mundari na mafarkin samun rayuwa mai inganci nan gaba. Galibinsu sun san yadda sauran sassan duniya suke ne kawai, ta hanyar hotunan da suke gani a wayoyinsu na salula. Ga alama fatansu ya kusa tabbata, domin Chaina za ta gina wani titin mota da zai hade Juba da Terekeka, kuma tazarar ba za ta wuce tafiya ta sa'a guda ba.