1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mumunar zanga zanga a Yemen

June 3, 2011

Fraministan Yemen,da kakakin gwamnatin,Da kuma shugaba Al Abdallah Saley sun samu raunika bayan da wata bam ta fashe a fadar shugaban ƙasa

https://p.dw.com/p/11Tno
Shugaba Ali Abdullah Saleh na YemenHoto: dapd

An bada rahoton cewa an sha mumunar arrangama a birnin Sanaa na ƙasar Yemen tsakanin dakarun gwamnatin da kuma na wasu mayaƙan dake goyon bayan wasu ƙabilu. Wannan gwabza wa da aka yi a sa'ilin da jam'ian tsaro suka barbazu a garin Taez dake a yanki kudu maso yammaci, inda suka riƙa yin harbi a sama domin hana masu zanga zagar ƙin jinin gwamnati tattaruwa bayan sallah juma'a ,ya biyo bayan tsagaita war da aka samu ta wasu yan sa'oi.

Masu aiko da rahotannin sun ce wata majiyar gwamnatin ta ce mutane da yawa suka samu raunika a ciki hada fraministan ƙasar da kuma kakakin majalisar dokoki yayin da wasu fudu suka mutu. Kuma wani gidan telbijan na yan adawa na ƙasar ya sanar da cewa shugaba Ali Abdallah Saley ya mutu a cikin hare haren .To sai dai wani dan jarida a birnin Sanaa ya ce ba tabbas akan wannan labari.ya ce baza a iya tabata da gaskiya wannan labnari ba ya zuwa yanzu, amma ya ce shugaba Ali Abdallah Saley ya samu Rauni.Bayan da aka harba wata iguwa a cikin wani masalaci dake cikin fadar shugaban ƙasar.

Kawo yanzu sama da mutane guda dari ne suka mutu a cikin zanga zangar ƙin jini gwamnati ta Ali Abdallah Saley wanda ke kan karagar mulki shekaru 33 da suka wuce.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal