1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Habasha ya dau hankali a jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala YB
November 2, 2018

Jaridar Die Tagesspiegel ta ce Abiy Ahmed ya karfafa zukatan 'yan Habasha a kasashen duniya. Firaministan na aiwatar da gagarumin sauyi a kasarsa wadda a baya ta yi kaurin suna da mulkin kama karya.

https://p.dw.com/p/37ZPm
Deutschland Afrika-Gipfel bei Bundeskanzlerin Angela Merkel
Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Sharhin jaridun na Jamus ya fara da jaridar Die Tagesspiegel, a sharhinta mai taken "Lakanin sa'a" Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya faranta wa magoya bayansa. Jaridar ta ce daruruwan 'yan kasar Habasha maza da mata dauke da tutocin kasar sun yi dafifi cikin murna da annashuwa da kade kade suna rera wakoki cikin harshen Amharic suka tarbi Abiy Ahmed a birnin Frankfurt a nan Jamus.

Mutane daga ko ina a cikin Turai suka yi gangami domin ziyarar, wasu 'yan kasar ta Habashan kimanin 20,000 wadanda ke gudun hijira a kasashen Sweden da Holland da ma nan Jamus sun jinjinawa gwarzonsu Firaminista Abiy Ahmed mai shekaru 42 da haihuwa a ziyarar kwanaki hudu da ya kai wasu kasashen Turai.

Deutschland Besuch Abiy Ahmed äthiopischer Premierminister
Abiy Ahmed na gaisawa da 'yan kasarsa a JamusHoto: DW/T. W. Erago

Jaridar ta ce Abiy Ahmed ya karfafa zukatan 'yan Habasha a kasashen duniya. Firaministan na aiwatar da gagarumin sauyi a kasarsa wadda a baya ta yi kaurin suna da mulkin kama karya. Ya sako fursunonin siyasa, ya kaddamar da shirin zaman lafiya da sasantawa da kasar Iritiriya makwabciyar kasarsa. Sannan ya raba mukaman ministoci daidai wa daida tsakanin maza da mata a majalisar zartarwar gwamnati.

A sharhinta mai taken gwamnatin Jamus na shirin karkata akalarta cinikayyarta daga Asiya zuwa Afirka, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ba da gudunmawar Euro biliyan daya ga Afirka domin habaka cinikayya.

Jaridar ta ce cinikayya da Afirka na da riba kamar yadda yake tattare da kasada. Gwamnatin Jamus na matukar sha'awar kulla kyakkyawar dangantaka mai armashi da makwabtanta na Afirka, ko ba dan komai ba, ta rage nauyi game da batun 'yan gudun hijira.

Deutschland Afrika-Gipfel bei Bundeskanzlerin Angela Merkel
Angela Merkel da bakinta a BerlinHoto: Reuters/A. Schmidt

A wani taron tattalin arziki a Berlin Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da gidauniyar Euro biliyan daya da za a sanya cikin asusun raya kasashen Afirka domin taimaka wa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa da harkokin kasuwanci da masana'antu. Wannan gidauniya za ta ba da kariya ga kamfanonin Jamus da za su yi hulda da Afirka ko da an sami tangarda wajen cinikayya a tsakanin kamfanonin na Jamus da Afirka.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci ne kan soke dokar mallakar kamfanonin ma'adanai a kasar Namibiya. Jaridar ta ce gwamnatin Namibiya ta soke dokar da ta bukaci cewa 'yan kasar ne kadai za su shugabanci kamfanoni ma'adinai a kasar. A ranar Asabar din da ta gabata ce gwamnatin ta soke dokar. Tun da farko dai dokar ta ce wajibi ne 'yan kasar bakaken fata su mallaki kashi 20 cikin dari na ma'adinai yayin da 'yan kasar waje na iya mallakar kashi biyar cikin dari. Tun dai a shekarar 2016 kasar ta fada matsalar koma bayan tattalin arziki.