1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi jana'izar Gorbachev a Moscow

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 31, 2022

A ranar asabar mai zuwa za a gudanar da jana'izar marigayi shugaban Tarayyar Soviet na karshe, kana gawarzon Jamusawa Mikhail Gorbachev da ya rasu yana da shekaru 91 a birnin Moscow na kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/4GHmV
Michail Gorbatschow
Marigayi Michail Gorbatschow da Jamusawa ke wa kallon gwarzonsuHoto: VASILY MAXIMOV/AFP/Getty Images

Kamfanonin dillanci labarai na Rasha, sun ruwaito cewa sun samu wannan karin bayani ne daga 'yar marigayi Gorbachev da kuma gidauniyarsa. Za dai a gudanar da jana'izar tasa a wani dakin taro mai cike da tarihi, wanda aka saba yi wa manyan tsoffin jami'an gwamnati bankwana gabanin binne su. Daga cikin fitattun mutanen da aka yi wa irin wannan bankwana, har da tsohon shugaban Tarayyar ta Soviet mafi dadewa marigayi Joseph Stalin da ya rigamu gidan gaskiya a shekara ta 1953. Sashen yada labarai na gidauniyar Gorbachev ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Interfax cewa, za a yi bankwana da marigayi Gorbachev tsakanin karfe 10 zuwa biyu na rana agogon Moscow, karfe 11 ke nan agogon GMT kafin a binne shi a ranar a fitacciyar makabartar da aka saba binne manyan jami'an gwamnati. Shugaba Vladmir Putin ne dai, zai jagoranci jana'izar ban girma ta kasa da za a yi wa marigayi Gorbachev din.