Ministocin EU sun bukaci warware rikicin Ukraine da Gaza
August 29, 2024Babban jami'in kula da harkokin waje na EU Josep Borrell, ya ce an shirya taron ne domin samar da mafita kan yake-yaken Ukraine da na Gaza har ma da dambarwar siyasar Venezuela.
Karub bayani: EU ta fitar da makudan kudi domin tallafawa Ukraine
Tun da fari dai an shirya gudanar da taron a Budapest na kasar Hungary, amma daga bisani ministocin suka karkata akalar taron zuwa birnin Brussels, domin nuna adawa da matakin Firaiministan Hungary Viktor Orbán na ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a watan Yuli.
Karub bayani: Kasashen EU za su yi taro a kusa da Ukraine
A yayin taron dai ministocin za su tattauna da ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan, kan dangantakar kasarsa da EU sannan a karkare da batun yakin Gaza da kuma rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar Venezuela da shugaba mai ci Nicolas Maduro ya yi ikirarin lashewa.