Jamus za ta ci-gaba da tafiyar da hulda da masar
June 3, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fada wa shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi cewa Jamus na adawa da hukuncin kisa da kasar Masar ke amfani da shi, wanda kuma wata kotu ke son a yanke wa tsohon shugaban kasar Mohammed Mursi da wasu 'ya'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi. Amma ta ce a shirye Jamus din take ta tafiyar da huldar kasuwanci da Masar. Merkel ta fadi wannan ne a wani taron menama labarai na hadin guiwa da ta yi da shugaban na Masar da ke ziyara a birnin Berlin.
"Za mu yi duk abin da za mu iya don bunkasa tattalin arzikin Masar mai yawan al'umma miliyan 90 akasari kuma matasa. Saboda haka Jamus da tke da kwarewa a fannonin fasaha da tattalin arziki, za ta taimaka wa ci-gaban Masar."
Da ma dai an yi ta takaddama game da ziyarar ta al-Sisi a Jamus.