1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel a bikin cikar DW shekaru 65

Usman Shehu Usman
June 4, 2018

Bikin ya bayyana tasirin shirye-shiryen tashar ta hanyar fadakarwa da ilmantarwa a ciki da wajen kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/2yutP
Bundeskanzlerin Angela Merkel und DW-Intendant Peter Limbourg beim Festakt 65 Jahre DW
Hoto: DW/J. Roehl

Taron da aka gudanar a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, ya samu halartar manyan 'yan siyasa da ministan cikin gidan da fannin al'adu da yada labari da kuma shugabannin daban-daban, inda babban darakatan DW Peter Limbourg ya bayyana irin ci gaba da tashar DW ke kara samu  musamman karuwar masu sauraro.

Mitarbeiterversammlung 2013 in Berlin Peter Limbourg
Babban darakatan DW Peter LimbourgHoto: DW

"Deutsche Welle na kaiwa ga karin jama'a fiye da ko wane lokaci, kuma muna samun kekkewan gamsuwa da ayyukanmu harma nan cikin gida kamar daga jam'iyyun kasar duk suna mutuntamu duk da babancin manufofin siyasarsu. Wannan ya faranta mana rai, sai dai fa hakan bai wadatar ba, muna bukatar kara zage damtse wajen isa ga masu saurarodomin sanar da su gaskiya. Kuma muna son kara fadakarda duniya abinda ke faruwa a Jamus da Turai baki daya"

Anata bangaren babbar bakuwa a bikin, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba da rawar da tashar DW ke takawa a fadin duniya. 

"Muna bayyana bukatun Jamus da Turai, a daukacin duniya an rungumi Jamus a matsayin kawa ta gaskiya. Da yawa cikin duniya sun sana sanin yadda al'amura ke gudana a cikin kasarmu da ma yadda ake rayuwa a Turai. Nuna wa jama'a yadda Turai ta ke dama sanar da abinda ke faruwa a duniya, musamman a yanzu da Birtaniya ke ficewa daga Turai, ina ganin a yanzu ayyukanku na da mahimmanci fiye da shekarun baya."

Deutschland Koalitionsverhandlungen von Union und SPD Monika Grütter
Minista a ma'aikatar al'adu da yada labarai a Jamus, Monika GrütterHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Minista a ma'aikatar al'adu da kafafen yada labarai na kasar Jamus, Monika Grütter ta yaba da yadda tashar ke tafiya da zamani.
"Idan muka duba kokarin da DW ta yi na tafiya da zamani, yadda suke hada Rediyo da Talabijin da kuma yada labarai a kafafen sadarwar zamani. Suna isar da sakonni ga kimanin mutane miliyan 170 a ko wace rana a fadin duniya, wadannan babban abin ci gabane kuma shi ne babban abin jinjinawa ga ma'aikatan na DW" 

Tasirin ayyukan DW ya dauki hankalin shugabannin duniya kamar Hamid Karzai tsohon shugaban kasar Agfanistan da ya halarci bikin cikar tashar shekaru 65.

FILE PHOTO - Former Afghan president Karzai speaks during an interview in Kabul
Tsohon shugaban kasar Afganistan, Hamis KarzaiHoto: Reuters/Omar Sobhani

"Kyakkyawan aiki a bada labarai da karin bayanai ga jama'ar duniya, ni abokin sauraron shirye-shiryen talabijin na DW ne kamarsu Euromax, Courdiriga da kuma Europe in consert."

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Claudia Juncker, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a bikin inda ya ce.

"Shirin Jamusanci na DW na burgeni matuka, kana DW suna da kololuwar kwarewar aikin jarida da kuma bada labarin ba tare da nuna bangaranci ba. Wannan babban abin jinjinawa ne."

Headerbanner 65 Jahre DW Deutsch

Da muryar shugaban kasar Jamus Theodor Heuss tashar Deutsche Welle ta fara watsa shirye shiryenta ta gajeran zangon radiyo daga birnin Kolon a ranar 3 ga watan Mayu shekara ta 1953. An fara yada shirye shiryen cikin harshen Jamusanci kadai, inda kuma daga baya aka kara harsunan kasashen ketare a farkon shekarar 1954. Sai a shekarar 1992 aka fara yada shirin tashar talabijin ta Jamusanci. Yanzu haka ana yada labarai cikin harsuna hudu a tashar talabijin ta DW, sannan harsuna 30 a radiyo da kafar Internet gami da karin bayanai ta kafofin sada zumunta na zamani. Kana akwai bangarren horas da 'yan jarida da ke aiki tun shekarar 1965, inda dubban 'yan jarida suka samu horo.Albarkacin bikin cika shekaru 65 majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta girmama tashar.