1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel na neman kafa gwamnati da wasu jam'iyu

Abdul-raheem Hassan
September 25, 2017

Kwana guda bayan kammala zaben gama gari na 'yan majalisun dokoki a Jamus, shugabar gwamnati Angela Merkel na fuskantar matsalar samun hada kan jam'iyyun da za ta yi kawancen kafa sabuwar gwamnati.

https://p.dw.com/p/2kfZj
Deutschland Bundestagswahl Merkel PK
Hoto: Reuters/F. Bensch

Babban kalubale da Merkel ke fuskanta dai kawo yanzu, shi ne yadda jam'iyyar kawancenta ta SPD ta fito fili karara ta bayyana yin hannun riga da ita a wannan tafiya tun bayan da hasashen sakamakon zaben ya nuna Merkel ta samun damar zarcewa karo na hudu a kan mulki. A yanzu zabi guda da ya ragewa shugaba Merkel, shi ne kafa gwamnatin da kananan jam'iyyu biyu.

Ana sa ran jam'iyar FDP da kuma The Green's za su kasance kan gaba wajen shiga tattaunawa da Merkel, a wani yunkuri na neman hadaka a kafa sabuwar gwamnatin. To sai dai kafa gwamnati da jam'iyyun na zama wani jan aiki da ke gaban shugabar ganin irin bambancin akida irin ta siyasa dake tsakanin su musamman jam'iyar The Green's mai kare muhalli da kuma CSU wace ke kawance da jam'iyar Merkel ta CDU.