1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

MDD za ta kada kuri'a kan harin 'yan Houthi a Baharmaliya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 10, 2024

Tun bayan fara yakin Gaza ne dai 'yan tawayen Houtin suka fara farwa jiragen ruwan, a matsayin martani ga luguden wutar da sojin Isra'ila ke yi wa yankin Zirin Gaza

https://p.dw.com/p/4b2uh
Hoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

A Larabar nan ce kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'ar yin tir da kuma bukatar dakatar da hare-haren da 'yan tawayen Houthi na Yemen ke kai wa jiragen ruwa na kasuwanci a tekun Baharmaliya.

Karin bayani:Dalilan 'yan Houthi na barazana a Bahar Maliya

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya rawaito cewa Amurka ce ta bukaci hakan, la'akari da yadda hare-haren ke neman tagayyara harkokin kasuwancin duniya, kasancewar kashi 12 cikin 100 na hada-hadar kasuwancin na duniya na wanzuwa ne ta wannan hanya.

Karin bayani:Iran ta tura jirgin yaki a tekun Bahr Maliya

Tun bayan fara yakin Gaza ne dai 'yan tawayen Houtin suka fara farwa jiragen ruwan, a matsayin martani ga luguden wutar da sojin Isra'ila ke yi wa yankin Zirin Gaza.

Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa dakarunta da na Burtaniya sun samu nasarar kakkabo jirage marasa matuka guda 21 da makamai masu linzami guda 3 da 'yan tawayen Houthi suka harba kan jiragen ruwa.